Majalisar dattijai ta cire sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume daga muƙamin mai tsawatarwa.
Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne a yau Laraba bayan ƙorafi da jam’iyyar APC, mai mulki ta yi kan wasu kalaman sanatan a baya-bayan nan.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto wata wasiƙar ƙorafi daga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma sakatarenta, Sanata Bashir Ajibola.
Wasiƙar jam’iyyar APC ta ce ta nemi a canza Sanata Ndume ne saboda kalaman da ya furta a kwanan nan.
Bayan karanta wasiƙar ne Sanata Akpabio ya nemi a kaɗa ƙuri’a domin amincewa ko watsi da buƙatar kuma daga ƙarshe sanatocin suka zaɓi tsige Ndume.
Nan take kuma aka zaɓi Sanata Tahir Munguno domin maye gurbin Sanata Ali Ndume.