fidelitybank

Majalisa ta titsiye shugaban kungiyar Malamai ta ASUU

Date:

Wasu mambobin majalisar wakilai, sun titseye shugaban ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, kan wasu zarge-zarge da ya yi na cewa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya yaudari ƙungiyar wajen jan hankalinta domin janyewa daga yajin aikin da ta shafe watanni tana yi.

Jaridar Daily Trust  ta ruwaito cewa, a wata hira da shugaban ASUU ya yi da wata jarida a ranar talata ya zargi Gbajabiamila da cewa, ya yi amfani da yaudara wajen sanya ƙungiyar janye yajin aikin da ta shafe wata takwas ta na gudanarwa a watan Oktoba.

Ta hanyar rubutaccen alƙawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta biya malaman duka albashin watannin da ta riƙe musu ba tare da ɓata lokaci ba.

Yayin da yake mayar da martani game da zargin na shugaban ASUU a Abuja, mai magana da yawun majalisar wakilan ƙasar Benjamin Okezie Kalu ya ce babu inda kakakin majalisar ya yi alƙawarin warware matsalar albashin da malaman ke bin gwamnatin tarayya bashi.

Inda ya ce, majalisar wakilan ta taimaka ne kawai wajen kawo ƙarshen yajin aikin, ta hanyar yin ƙoƙari wajen inganta albashin malaman jami’o’in tare da taimakawa wajen samar da kuɗin inganta jami’o’in ƙasar.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp