fidelitybank

Majalisa ta tirsasa Bosun ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri bayan tantance shi

Date:

‘Yan Majalisar Dattawa, sun tilasta wa Dr. Bosun Tijani neman afuwarsu da kuma ‘yan Najeriya game da wasu kalamai da ya yi a shafukan zumunta a baya.

Dr. Tijani na cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika wa Majalisar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa, wanda ɗan jihar Ogun ne.

Sanatocin sun karanto irin saƙonnin da ya wallafa a Twitter, cikinsu har da na 2019, inda ya ce “ba na alfahari da riƙe fasfo ɗin Najeriya da kuma Najeriya a matsayinta na ƙasa”.

Haka nan, an karanto wani saƙon da ya kira ‘yan Majalisar “shashashai” game da yadda suke tantance ministoci.

Mista Tijani bai musanta zarge-zargen ba.

Bayan sanatoci da dama sun yi magana, masu goyon bayansa da masu neman ƙarin bayani, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya umarce shi da ya nemi afuwarsu kafin su ƙyale shi ya tafi.

“Ina neman afuwarku ‘yan Majalisa da ma sauran Najeriya kan waɗannan abubuwan da na faɗa,” in ji shi. “Ina so ku lura da dalilan da suka sa na yi su, ban yi su don na ɓata sunan wani ba.”

Daga nan ya rusuna kuma ya sauka daga kan dandamali.

pulse news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp