fidelitybank

Majalisa ta Tara ta karɓi ƙorafi 705 cikin shekaru 4 – Lawal

Date:

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya mai barin gado, Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce Majalisa ta Tara da ya jagoranta ta karɓi ƙorafi 705 daga ɗiɗaikun ‘yan ƙasar cikin shekara huɗu.

Da yake jawabin bankwana a ranar Asabar a zauren Majalisar, Ahmad Lawan ya ce sun samu ƙorafi 146 a shekarar farko, 239 a shekara ta biyu, 232 a shekara ta uku, da kuma 88 a ta uku.

“Dukkansu suna matakai daban-daban na samun biyan buƙata,” in ji shi.

Kazalika, ‘yan Majalisa ta Tara sun gabatar da ƙudiri 361 (motion) sannan kuma suka ɗauki matsaya (resolution) 488 a kan batutuwa daban-daban da suka ja hankalin gwamnati a kansu, a cewarsa.

“Kwamatocin sa-ido na Majalisa ta Tara sun kai ziyarar aiki 371 zuwa ma’aikatu da sashe-sashe da hukumomi da kuma wuraren gudanar da ayyuka a faɗin ƙasa,” kamar yadda ya bayyana.

A ranar Talata mai zuwa ake sa ran za a rantsar da Majalisa ta 10, yayin da ake ci gaba da tafka siyasa game da wanda zai maye gurbin Ahmad Lawan a matsayin shugaba.

Jam’iyyar APC mai mulki dai na son ‘yan majalisar su zaɓi Godswill Akpabio daga Jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya, a matsayin shugaba, da kuma Barau Jibrin daga Kano a arewacin ƙasar a matsayin mataimakinsa.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp