Majalisar Dattawa, ta tantance Dr Mariya Mairiga Mahmoud a matsayin minista daga jihar Kano.
Dr Mariya dai ita ce ta maye gurbin Maryam Shetty da shugaba Tinubu ya cire sunanta a satin daya gabata.
Sauyan sunan Maryam Shetty da Dr Mariya Mairiga ya janyo ce-ce-ku-ce shafukan sada zumunta.