Duk da sukar da ake yi mata, majalisar dattawa a ranar Talata, ta tabbatar da nadin mataimakiyar shugaban kasa ta musamman kan sabbin kafafen yada labarai, Lauretta Ifeanyi-Onochie a matsayin babbar shugabar hukumar raya yankin Neja Delta.
Majalisar dattijai a zauren majalisar ta kuma tabbatar da wasu mutane 12 biyo bayan tantance wadanda aka nada a ranar Juma’ar da ta gabata a harabar majalisar dokokin kasar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da nadin mataimakiyarsa ta musamman kan sabbin kafafen yada labarai, Lauretta Ifeanyi-Onochie a matsayin babbar shugabar hukumar raya yankin Neja Delta, lamarin da ya janyo yabo da tofin Allah tsine a wasu bangarori.
Buhari ya kuma bayyana sunayen wasu mutane 14 a cikin wasikar a matsayin Manajan Darakta, Daraktoci da membobin hukumar.
Sun hada da Samuel Ogokwu, daga Jihar Bayelsa, a matsayin Manajan Darakta, wanda zai yi wa’adin shekaru biyu don kammala wa’adin mulkin da ya gabace shi.
Haka kuma jerin sunayen sun hada da Dimgba Erugba, mai wakiltar jihar Abia, Dr. Emem Willcox Wills (Akwa Ibom), Dattijo Denyanbofa Dimaro (jihar Bayelsa), Hon. Orok Duke (Cross River) da Dr. Pius Odudu (Jihar Edo).
Injiniya Anthony Ekenne, (Jihar Imo), Hon. Gbenga Edema (Jihar Ondo), Elekwachi Dimkpa (Jihar Rivers), Alhaji Mohammed Kabir Abubakar, (Jihar Nasarawa, mai wakiltar shiyyar Arewa ta tsakiya), Alhaji Sadiq Sami Sule – Ikoh (jihar Kebbi, Arewa-maso-Yamma) da kuma Farfesa Tahir Mamman SAN. , (Jhar Adamawa, Arewa maso Gabas)
Shugaban ya kuma zabi Manjo-Janar Charles Airhiavbere (rtd) daga jihar Edo a matsayin (Babban Darakta, Kudi) da Charles Ogunmola, daga jihar Ondo, a matsayin Babban Daraktan, Projects shi ma ya sanya jerin sunayen wadanda aka nada a NDDC.