Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da harkokin waje, ya musanta zargin da wani dan majalisar Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya yi na almundahana a harkar aikin Hajji.
Shugaban kwamitin Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ne ya musanta zargin a wata hira da BBC.
Shugaban kwamitin ya ce ya tun da farko ya shirya sauraron jin ra`ayin jama`a kan hukumar alhazan kasar da kyakkyawar niyya ta neman shawarwarin da za su taimaka wajen inganta ayyukanta.
A wata hira da yayi da BBC a karshen mako dan Majalisar Dattijai mai wakiltar Sokoto ta Kudu Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya yi zargin cewa wani bincike da ya gudanar ya gano ana almundahana a harkar aikin Hajji.
Ya ce “binciken ya gano ana sama da fadi da kudaden mahajjata, otel da ya kamata a kama na kwana arba’in sai a kama na tsawon kwana casa’in sauran kwanakin kuma sai a sanya Larabawa a dakunan bayan alhazai sun tafi, sai a raba kudin tsakanin masu otel da kuma shugaban Hukumar Alhazai na wancan lokacin inda otel zai dauki kashi 25 shi kuma shugaba ya dauki kashi 75” a cewar Sanata Dan Baba.