Majalisar dattawa ta musanta ikirarin da ake na cewa tana shirin amincewa da sayan jiragen saman shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Obot Akpabio ya musanta rahotannin da aka yi ta yadawa a kafafen yada labarai na cewa Majalisar Dattawa na shirin samar wa Tinubu da Shettima sabbin jiragen sama.
Da yake zantawa da ‘yan jarida a Maiduguri jim kadan bayan ya jagoranci tawagar da suka kai wa Sanata Tahir Monguno ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa, Akpabio ya kawar da gaskiya a cikin rahoton.
A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana a kafafen yada labarai cewa Shugaban Majalisar ya yi tsokaci cewa Majalisar za ta amince da sayen sabbin jiragen sama ga shugaban kasa da mataimakinsa ba tare da la’akari da yadda ‘yan Najeriya ke fama da yunwa ba.
Shugaban majalisar dattawan ya ce rahoton ya fito ne daga masu yada farfaganda da kuma marubuta na biyar, yana mai jaddada cewa majalisar ta mayar da hankali ne wajen samar da dokar da za ta goyi bayan aiwatar da ajandar sabunta bege na Shugaba Tinubu.
Akpabio, wanda ya bayyana jin dadinsa da halin tsaro da jihar Borno ke ciki a halin yanzu, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu’a.
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa, “Ina so in karyata rade-radin da kuke ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya ce zai saya wa Shugaban kasa da Mataimakinsa sabon jirgin sama, ba tare da la’akari da cewa ‘yan Najeriya na fama da yunwa ko ma dai ba.
“Ban taba fadin haka ba. Na kasance a Zanzibar, Tanzaniya, aikin hannun masu yada farfaganda ne da marubuta na biyar, waɗanda ba su taɓa ganin wani abu mai kyau a cikin abin da muke yi ba. Ka huta, yi wa gwamnati addu’a, a yi hakuri, ka tabbatar da cewa hadakar Tinubu da Shettima zai kawo arziki da wadata ga kowa.
“Na yi farin ciki da ganin zaman lafiya ya dawo Borno, sakamakon kwazon da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi. Ina so in gaya wa mutanen Borno nagari da su ci gaba da marawa gwamnati baya.”