Majalisar dattijai ta tura wa shugaba, Bola Tinubu, sunayen mutum 45 da ta amince ya naɗa su ministoci, daga cikin mutum 48 da ya nemi ta tantance.
Mai taimaka wa shugaba Tinubu na musamman kan harkokin majalisar, Abdullahi Gumel ya ce hakan na nufin majalisa ta kammala aikin da ya kamata ta yi game da tantance sunayen ministocin.
A ranar Litinin Majalisar Dattawa ta kammala tantance ministocin, inda ta sanar da cewa akwai mutum uku da ta jingine tabbatar da su saboda bai wa hukumomin tsaro damar kammala aikin da suke yi a kansu.
Mutum ukun da majalisa ba ta tabbatar da naɗin nasu ba sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da Sanata Abubakar Danladi da kuma Stella Okete.