Majalissar dokokin jihar Edo ta umarci mataimakiyar shugabar masu rinjaye na majalisar, Natasha Osawaru, da ta fice daga zauren majalisar bisa sanya suturar da ba ta dace ba.
Kakakin majalisar, Blessing Agbebaku, ta umurci ‘yar majalisar mai wakiltar mazabar Egor da ta fice daga zaman majalisar, biyo bayan umarnin da Nicholas Asonsere, mai wakiltar mazabar Ikpoba Okha ya gabatar.
A nasa jawabin, Asonsere ya ce, salon sanya tufafin mataimakiyar shugaban masu rinjaye ya sabawa ka’idojin majalisar.
Ya kuma ce, zauren majalisar ba zai amince da kyale mata na shiga irin yadda suka ga dama ba bisa yadda wajen ke da mutunci.