Majalisar dattawa ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike, don sanin inda aka kwana a aikin gyara matatun man fetur na ƙasar.
Binciken zai haɗa da ɗimbin kudin da aka kashe da sunan gyaran tun daga shekara ta 2010 zuwa 2023, wanda ake zargin ya kai fiye da naira tiriliyan 11.
‘Yan majalisar sun ce ba daidai ba ne a ce gwamnati ta kashe irin wannan kuɗi mai yawa ba tare da samun biyan bukata ba.
Sanata Kawu Sumaila ya halarci zaman majalisar, kuma ya yi wa Ibrahim Isa ƙarin bayani kan muhawarar da suka yi a zaman.


