Majalisar wakilai ta kaddamar da bincike kan yadda Nadeem Anjarwalla, Shugaban Binance na yankin Africa ya kubuta daga hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Kudurin ya biyo bayan kudirin da Dennis Okafor ya gabatar da shi a ranar Laraba r nan yayin zaman majalisar.
Idan dai za a iya tunawa, an tsare Mista Anjarwalla da Tigran Gambaryan a Abuja kafin ya tsere daga gidan ajiya da gyaran hali, daga bisani kuma ya fice daga kasar nan.
A cikin kudirin, Okafor ya ce, tserewar Anjarwalla daga gidan yari abin kunya ne ga Najeriya.
Ya kuma roki majalisar da ta binciki lamarin da ya kai ga ya cika wndon sa da iska.
A halin da ake ciki, majalisar ta kuma musanta zargin neman cin hancin da rashawa daga hannun wasu mutane da aka yi ikirari.
Shi kuwa Kama Nkem Kanma, ya yi tsokaci kan batun, inda ya bayyana cewa majalisar ba za ta iya jure wannan abun kunyar ba.
Ko da yake dan majalisar bai ambaci kamfanin Binance ba, duk da a baya ne dai shugaban kamfanin na Binance Richard Teng ya zargi wasu ‘yan majalisar da neman cin hanci daga hannunsu.
Teng, a cikin wani sako da ya wallafa a shafin X ranar Talata, ya zargi kwamitin majalisar wakilai kan laifukan kudi da neman nagoro daga hannun kamfanin na Binance.
Kanma ya ce majalisar ba ta taba yin irin wannan bukata daga Binance ba kuma ta yi kira da a dauki kwakkwaran mataki.
Da yake yanke hukunci kan batun, kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya umarci magatakardar majalisar, Yahaya Danzaria da ya yi amfani da kafafen yada labarai wajen karyata ikirarin.