Batun shugabancin majalisa ta goma na ci gaba da jan hankula da kuma haifar da turka-turka tsakanin ‘ya’yan jam’iyya mai mulki a Najeriya har ma da ‘yan adawa.
A wannan lokaci ƴan majalisar wakilai masu jiran gado musamman na jam’iyyar APC ne suka ce, ba sa goyon bayan da matsayin uwar jam’iyyar ta ɗauka na bayar da sunan waɗanda take so su kasance shugaban majalisar da mataimakinsa.
‘Yan majalisar ƙarƙashin wata ƙungiya da suka kira ‘New Vision 10th Assembly’ wadda ta ƙunshi sababbin ‘yan majalisa daga dukkan jam’iyyu sun ce zaman majalisar lafiya shi ne, a bar ‘yan majalisa da kansu, su zaɓi wadanda suke so su shugabance su.
A farkon makon nan ne, jam’iyyar APC ta fitar da sunan Hon Tajuddeen Abbas daga jihar Kaduna da kuma Hon. Benjamin Kalu daga Abia a matsayin waɗanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ke goyon bayan a zaɓe su matsayin shugaba da mataimakinsa.