fidelitybank

Majalisa ta gayyaci shugaban Kwastom

Date:

Kwamitin Majalisar Wakilai kan karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a, ya gayyaci babban kwanturolun hukumar kwastom, Adewale Adeniyi, domin ya yi mata bayani kan abin da ya sa wasu manyan jami’an hukumar suka ƙi yin ritaya duk kuwa da lokacinsu ya yi.

Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko ya fitar, ya ce an gayyaci babban jami’in hukumar ne domin ya yi bayani kan ƙorafin da aka shigar wa kwamitin dangane da ƙin yin ritaya da wasu manyan jami’an hukumar suka yi bayan lokacinsu na hakan ya yi.

Gidauniyar Obasi-Pherson Help ce ta shigar da ƙorafin gaban kwamitin , inda ta yi zargin cewa wasu jami’an hukumar masu muƙamin mataimakin kwanturola da masu muƙamin kwanturola sun ƙi ajiye aikinsu, bayan cikar lokacin.

Yayin bayar da sammacin, majalisar wakilan ta ce babban kwnturolan ƙasar ne kaɗai ke da haƙƙi bayyana wa ‘yan ƙasa ainihin gaskiyar wannan zargi.

“Ƴan Najeriya sun cancanci sanin gaskiyar abin da ya faru daga bakin babban konturolan…, a wannan lokaci da mafi yawan matasanmu ke neman ayyukan yi, indai batun nan gaskiya ne, to babu adalci ace ga wasu tsofaffin da suka isa ritaya su ƙi yin hakan,” a cewar shugaban kwamitin, Mike Etaba.

Ya ƙara da cewa ”ba wai muna ɗaukar ɓangare ba ne, muna nazarin kowane batu ne bisa gaskiya domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka cancance shi”.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp