fidelitybank

Majalisa ta gayyaci Ministan Lantarki da hukumar NERC

Date:

Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ya gayyaci ministan lantarki, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar NERC da su bayyana gabansa a wani zaman bincike da za a yi game da ƙarin kuɗin lantarkin da aka yi a baya-bayan nan.

Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ne ya bayyana haka yayin gudanar da ayyukan kwamitin da kuma kai ziyara zuwa ma’aikatar lantarki da ke Abuja.

Abaribe ya ce majalisar dattawa tuni ta amince a yi zaman ranar 29 ga watan Afrilu inda hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi.

Ministan ya bayyana tarin matsalolin da suka addabi ɓangaren lantarki a Najeriya da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da rashin iskar gas inda ya buƙaci kwamitin da ya tallafa wa ma’aikatar lantarki domin cimma ƙudurorinta.

Kwamitin majalisar ya kuma duba wani aikin samar da wuta a harabar ma’aikatar. Sanata Abaribe ya kuma bayyana damuwa kan duk da maƙudan kuɗin da ake zubawa a ɓangaren lantarki, masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokawa kan matsalolin da ake fuskanta.

Ya kuma nemi sanin dalilin da ya sa kamfanin samar da wutar lantarki da sauran hukumomi da ke ɓangaren wutar ke bari babban layin wutar lantarki ke yawan lalacewa cikin shekaru.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp