fidelitybank

Majalisa ta gayyaci Ministan kuɗi a kan ɓatan kuɗaɗen man fetur

Date:

Kwamitin majalisar wakilai da ke bincike kan zargin ɓatan kuɗin man fetur, ya gayyaci ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed, da Sakataren gwamnatin tarraya Boss Mustapha, da kuma ministan shari’a Abubakar Malami.

Yana neman su bayyana gabansa a wani ɓangare na binciken da yake yi.

Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah ne ya bayar da umarnin gayyatar jami’an gwamnatin, bayan kwamitin ya koma sauraron bahasi kan zargin ɓacewar kuɗin gangar man fetur miliyan 48 da aka sayar wa China da wasu masu kwarmata bayanai suka bayyana.

Karanta Wannan: Buhari ya kai ziyara masallacin Annabi S.A.W

Kwamitin na bincike ne kan zargin ɓatan sama da dala biliyan 2.4 na man fetur da aka fitar ba bisa ƙa’ida ba, domin sayar da shi, tun daga shekarar 2014 zuwa yau.

Mista Gbillah ya ce kwamitin ya ba da umarnin ne domin sanin irin rawar da – ma’aikatar kuɗi da sauran hukumomin gwamnati – suka taka musamman kan abin da ya shafi tsarin masu kwarmata bayanai.

”Mafi yawan matsalolin – abin da ya kamata mu bincika game da tsarin masu kwarmata bayanai – na tasowa ne tsakanin ma’aikatar kuɗi da ofishin ministan shari’a”.

Tun da farko kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila wanda ya samu wakilcin Isiaka Ibrahim Ayokunle, ya nuna damuwa game da raguwar kuɗin shiga da ƙasar ke samu daga sayar da ɗanyen man fetur.

Ya ce abu ne mai tayar da hankali zargin da masu kwarmata bayanan suka yi cewa fiye da dala biliyan 2.4 na kuɗin gangar mai miliyan 48 ne suka ɓace a ƙasar.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...
X whatsapp