Kwamitin wucin gadi kan matsalolin tsaron jihar Filato na Majalisar Wakilan Najeriya ya gayyaci gwamnan jihar Caleb Mutfwang da tsaffin gwamnonin jihar da sauran masu ruwa da tsaki na jihar zuwa wani babban taro da nufin lalubo hanyar magance hare-haren da jihar ke fuskanta a jihar.
Jaridar Dailu Trust ta ambato shugaban kwamitin, Hon. Dr Wale Hammed na cewa matakin wani yunƙuri ne na ɗaukar matakan da suka dace domin magance kashe-kashen da jihar ke fuskanta.
A baya-bayan jihar – wadda ke tsakiyar Najeriya – ta fuskanci hare-haren da faÉ—an Æ™abilanci da ya haddasa asarar rayuwa da dukiyoyi masu dimbin yawa.
Dakta Hammed ya ce yana fatan taron – wanda ya Æ™unshi duka masu ruwa da tsaki na jihar – zai kawo Æ™arshen matsalar da ta jima tana ci wa jihar tuwo a Æ™warya.
Cikin wata hira da BBC Hausa a makon da ya gabata, Gwamna Jihar Caleb Muftwang ya alaƙanta rikice-rikicen da jihar ke yawan fama da su, da gazawar hukumomi, wajen hukunta masu haddasa rikicin da ya-ƙi-ci-ya-ƙi-cinyewa.