Majalisar dattawa ta mikawa gwamnan babban bankin kasa CBN, Olayemi Cardoso, sammace a kan faduwar darajar Naira da kuma hauhawar farashin kayayyaki da kasar nan ke fuskanta.
Wannan sammacin ya fito ne ta hannun kwamitin dake kula a kan harkokin banki da inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a karkashin Sanata Adetokunbo Airu.
An bukaci gwamnan da tawagarsa da su bayyana a ranar Talatar makon gobe, domin bayyana halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki da kuma yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa wanwar a kasuwar hada-hadar kudi.
Kwamitin a wani taro a ranar Larabar nan, ya nuna damuwarsa kan yadda darajar Naira ta yi kasa, yayin da kudin dalar Amurka ya kai Naira 1,520 kamar yadda ya faru a ranar Larabar nan.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron da aka gudanar a bayan fage a zauren majalisar, Sanata Airu ya ce halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, musamman ma hauhawar farashin kayayyaki yana da matukar damuwa ga ‘yan majalisar.
Ya ce, sun gudanar da taro a yammacin yau, domin mayar da hankali kan alkiblar tattalin arzikin kasar nan.