fidelitybank

Majalisa ta dukufa kan bacewar Bindigun ‘Yansanda dubu 178

Date:

Majalisar Dattawa na bincike kan rahotonnin ɓacewar fiye da bindigogi 178,000, yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar wasu yankunan ƙasar.

Haka kuma majalisar ta ce za ta gudanar da bincike kan rarraba kwangilar sayen makamai da ya kai na naira biliyan 1.1, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Cikin wani rahoton bincike da ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙasar ya gabatar wa majalisar a 2019, ya ce ya gano yadda aka rarraba kwangilar sayen makaman.

Rahoton ya bayyana cewa “a watan Disamban 2018 akwai bindigodi 178,459 ciki har da ƙirar AK-47 88,078 da ba a san inda suke ba.

Haka ma zuwa watan Janairun 2020, aƙalla bindigogi da pistol 3,907 ne suka ɓata.

Ƴan majalisar dattawan sun ce suna fargabar bindigogin su faɗa hannun ɓata-gari, da ke ƙara dagula matsalar tsaro musamman a ƙasar da ke fama da rikicin Boko Haram da ƴanfashin daji da masu garkuwa da mutane.

Yayin da yake jawabi a madadin Babban Sifeton Ƴandan ƙasar, Mataimakan sifeton ƴansandan ƙasar, AIG Abdul Sulaiman ya ce wasu daga cikin bindigogin an sace su ne a lokacin fashi da hare-haren da ake kai wa ƴansanda.

Ya kuma buƙaci kwamitin majalisar dattawan ya ba shi ƙarin lokaci, domin gabatar da cikakken rahoto kan bindigogin da ba a san inda suken ba.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp