fidelitybank

Majalisa ta buƙaci a ci tarar Ƴan Daudu ko a ɗaure su a gidan Yari

Date:

Wani ƙudiri da aka gabatar a gaban Majalisar Wakilai ta ƙasa da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi kwadkwarima ya nemi a haramta Ɗan Faudu a ƙasar.

Da yake karanto sashe na 4 na dokar ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal, ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a ɓoye.

Ya nemi a saka ɗaurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar Naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin ɗan daudu.

Ɗan majalisar na so a ƙara wani ƙaramin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: “Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000.”

A jiya Talata ne ‘yan majalisar suka yi wa ƙudirin karatun farko. Sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kashe-kashen Benue

Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana...

Ba dan mun yi wa Iran barna ba da har yanzu ba ta nemi sulhu ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada cewa harin...

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan masu leken asiri

Kamfanin dillancin labarai na sashen shari'a a Iran ya...

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...
X whatsapp