Majalisar dattijan Najerya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta haɗa kai da wasu kasashe domin yin kira a tsagaita bude wuta a rikicin Isra’ila da Hamas.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoba ne sojojin Isra’ila suke yin ruwan bama-bamai a Gaza, bayan mayaƙan Hamas sun ƙaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 a Isra’ila, waɗanda mafi yawansu fararen hula ne, a cewar hukumomin Isra’ila.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas, adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya zarce mutum 10,000 ciki har da yara sama da 4,000.
A wani kudiri da Sanata Abdulrahman Kawu daga Kano ta Kudu ya gabatar a ranar Talata, Majalisar Dattawar bayan muhawara mai zurfi ta bayyana mace-mace da kuma adadin waɗanda suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Isra’ila da Hamas a matsayin abin tsoro.
Yayin da suke bayyana ra’ayinsu, ƴan majalisar sun yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a bangarorin biyu, sannan suka buƙaci a zauna lafiya domin kauce wa abin da zai kawwo yaɗuwar rikicin.
Wannan kiran na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙara jaddada buƙatar tsagaita wuta cikin gaggawa, inda ta bayyana Gaza a matsayin makabarta ga kananan yara yayin da adadin wadanda suka mutu ya haura 10,000.