Majalisar wakilai ta kasa ta bukaci hukumar kwastan da ta biya diyyar ran mutanen da jami’anta suka kashe da wadanda suka raunata a fadin Najeriya jumullar Naira miliyan 390.
Wannan na cikin shawarar da ke kunshe a rahoton kwamitin majalisar mai kula da harkokin hukumar kwastan, bayan binciken da ‘yan kwamitin suka gudanar kan abin da ya faru a jihar Katsina da kuma jihar Oyo.
Kwamitin ya bayar da shawarar biyan kowane daya daga mutane 10 da ake zargin kwastan sun kashe a Jibia, jihar Katsina ranar 9 ga watan Agusta 2021, a kan diyyar Naira miliyan 20 kowanne daga cikinsu.
Su kuwa mutane 13 da suka samu raunuka a lamarin, a biya su Naira miliyan bibbiyu domin jinya.
Kan rikicin Iseyin a jihar Oyo kuwa, majalisar ta bukaci hukumar kwastan ta biya diyyar mutane hudu da ake zargin jami’anta sun kashe, suma Naira miliyan 20 kowanne, wadanda suka ji rauni kuwa a biya su Naira miliyan biyu kowa.
Majalisar ta nemi a gurfanar da jami’an kwastan din da suke da hannu a kisan ‘yan Najeriya wadanda ba su ji ba ba su gani ba, a gaban shari’a domin a hukunta su ya zama izin ga sauran.