fidelitybank

Majalisa ta bukaci gwamnati ta rinka baiwa dalibai masu “first class” aiki kai tsaye

Date:

Majalisar wakilai ta bukaci ma’aikatu da sassa da hukumomi da su baiwa ‘yan Najeriya da suka kammala karatun digiri da sakamakon mafi kyau na first class a cibiyoyin Najeriya aiki kai tsaye.

An cimma matsayar ne a ranar Laraba bayan amincewa da kudirin da Chinedu Martins ya gabatar.

A cikin yunƙurin, Martins ya ce, akwai ɗaruruwan ɗalibai masu sakamako na first class na ta gararanba a kan titi ba tare da aikin yi ba.

Ya lura cewa, ɗaliban suna samun nasarar ta hanyar “ƙoƙari mafi girma, aiki mai juriya, ƙuduri, da sanya damuwa.”

Ya jaddada cewa, akwai alaka tsakanin rashin ci gaban Najeriya da kuma yadda ake gujewa wadanda suka kammala digiri da sakamako mafi kyau

“Rashin kasawar Najeriya barin matsayin “kasa mai tasowa”, mai yiwuwa ba zai rasa nasaba da rashin hankali da rashin kishin siyasa na masu mulki da masu tsara manufofin bullo da tsarin bayar da lada ta hanyar da mafi kyawun kwakwalwa za su mamaye muhimman mukamai kai tsaye a cewarsa, zuwa yankin iyawar su,” in ji Martins.

Mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase ya nuna adawa da kudirin a kan cewa ya kamata a karfafa wa daliban da suka kammala karatun digiri na daya kwarin guiwa su dauki manyan ayyuka a duniya.

Ya bayyana cewa hukumomi da yawa suna da mafi ƙarancin ƙa’idodin da suke amfani da su wajen tantance aiki ga manyan MDAs.

Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, a lokacin da yake mayar da martani kan kalaman mataimakinsa, ya ce, hukumomi da dama na daukar ma’aikata masu sakamako na 3 wato third class aiki, yayin da masu sakamako na first class ke yawo a kan tituna.

Bayan doguwar muhawara, majalisar ta amince da kudurin.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...

Isra’ila ta kashe Manyan Jami’an Iran biyar a hare-hare

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp