Majalisar dokoki ta bai wa Dangote da BUA da IBETO da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin kwanaki 14 da su gurfana a gaban kwamitin hadin gwiwa na Majalisar kan tsadar farashin siminti a kasar nan.
Hakan ya biyo bayan gazawar da kamfanonin da wasu suka yi wajen gurfana a wajen zaman binciken da aka yi ranar Talata.
An dai kafa kwamitin hadin gwiwar na majalisar dokokin, wanda ya kunshi kwamitocin majalisar masu kula da ma’adanai da kasuwanci da masana’antu da kuma ayyuka na musamman, domin ‘binciken ƙarin farashin siminti a kasar nan ba bisa ka’ida ba, da kamfanonin yin simintin suka yi.
Majalisar ta kuma gayyaci ministan ma’adanai na kasa, Dele Alake, da ya gurfana a gaban kwamitin bayan ya kasa bayyana a ranar Talata.
Majalisar ta kuma ba da umarnin cewa, ministan ya bayyana ranar Talata, 21 ga watan Mayu Dangote da BUA da IBETO da dai sauran, su bayyana a ranar Litinin.