Majalisar dattawa ta amince da ƙudurin babban bankin ƙasar nan na sake fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar.
Majalisar ta amince da ƙudurin bayan zazzafar muhawara kan ƙudurin da Sanata Uba sani ya gabatar a zauren kan ƙudurin babban bankin na sake fasalin wasu takardun kudin ƙasar.
Mafiya wayan ‘yan majalisar sun amince da ƙudurin, to sai dai wasu daga ciki sun bayyana damuwarsu game da ranar da babban bankin ya saka na daina karɓar tsoffin kuɗin a faɗin bankunan ƙasar.
Sannan kuma sun ɗiga ayar tambaya kan da alfanun yin hakan game da tattalin arziki, da yadda yin hakan zai sauƙaƙa hauhawar farashin kayyaki da farfaɗo da darajar naira.
Suna masu buƙatar gwamnan babban bankin Godwin Emefiele da ya yi musu ƙarin haske kan waɗannan batutuwa.
‘Yan majalisun sun kuma ce suna fargaba game da illar da hakan za ta haifar ga mazauna karkara da wauraren da ba su da bankuna.
A sanarwar da babban bankin ya fitar game da sake fasalin kuɗin ya ce sabbin kuɗin za su fara yawo daga ranar 15 ga watan Disamban 2022, a yayin da za a daina karɓar tsoffin kuɗin ranar 31 ga watan Janairun 2023.