Majalisar dattawaa ta amince a riƙa cire kashi 15 na kuɗaɗen gudanar da ma’aikatar raya yankunan ƙasar daga asusun jihohin ƙasar.
A ranar Alhamis ne Majalisar ta amince da ƙudirin bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar kan ayyuka na musamman, wanda shugaban kwamitin Sanata kaka Shehu ya gabatar.
Wannan batu dai ya haifar da zazzafar muhawara a zauren majalisar, inda wasu ‘yan majalisar suka nuna adawa da matakin.
Sanata Yahaya Abdullahi, daga jihar Kebbi ya ce matakin zai sa gwamnatocin jihohi su yi ta shigar da gwamnatin tarayya ƙara, saboda a cewarsa babu jihar da za ta so a riƙa yanke mata kuɗi da nufin ɗaukar nauyin wata ma’aikata ta tarayya.
To sai dai mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano ya kore fargabar takwaran nasa.
Yana mai cewa ba wai yanke kuɗaɗen jihohin za a yi ba, a maimakon haka kashi 15 cikin 100 na gudanar da ma’aikatar jihohin za su bayar, yayin da gwamnatin tarayya za ta bayar da ragowar.
A ranar Laraba ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanar da kafa sabuwar ma’aikata da za ta kula da sauran hukumomin raya yankuna, bayan rushe ma’aikatar raya yankin Naija Delta.
A yanzu ƙasar na da hukumomin raya yankuna da suka haɗa da ta yankin Naija Delta da ta arewa maso gabas da ta arewa maso yamma, da kuma ta kudu maso gabas.