Masu neman kujerar kakakin majalisar wakilan Najeriya guda biyu Hon. Aliyu Betara da Hon. Yusuf Gagdi sun janye wa Tajudeen Abbas don zama kakakin majalisar wakilan kasar ta 10.
Betara da Gagdi sun bayyana janye takarar tasu ne jim kaɗan bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, ranar Lahadi.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna mataimakin shugaban kasar Sanata Kashim Shettima na tabbatar da batun janyewar Betara da Gagdi.
Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar dai na mara wa Hon. Tajuden Abbas da Benjamin Kalu don zama kakakin majalisar da mataimakinsa, a ƙunshin majalisar wakilan ƙasar ta 10.
A ranar Talata 13 ga watan Yuni ne za a ƙaddamar da sabuwar majalisa ta 10 a ƙasar, bayan babban zaɓen ƙasar da aka gudanar cikin watan Fabrairun da ya gabata