fidelitybank

Majalisa na shirin janye dakatarwar da ta yi wa Ningi – Akpabio

Date:

Shugaban Majalisar Dattijai , Godswill Akpabio, ya ce a kusa majalisa za ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi mai wakintar Bauchi ta tsakiya a jam’iyyar adawa ta PDP.

Jaridar Daily Trusrt ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne ƙasa da awa 24 da ɗan majalisar ya aike wa Akpabio da wasiƙa wadda ciki ya yi masa barazanar ɗaukar matakin shari’a kan dakatarwar da aka yi masa idan ba a janye ta ba nan da mako guda.

An dakatar da Ningi ne bayan wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa wadda cikinta ya yi zargin cewa akwai naira tiriliyan sama da uku da aka cusa a cikin kasafin kuɗi ba tare da an yi bayanin me za a yi da ita ba.

Bayan wata doguwar muhawara da aka yi a majalisar mai kama da titsiye, an sanar da dakatar da Ningi watanni uku kuma an nemi ya rubuta wasikar neman afuwa saboda ‘ɓata wa majalisar suna da ya yi’ in ji Shugabanta.

Cikin wasiƙar da lauyan Ningi ya rubuta, Femi Falana ya ce Ningi ya zargi Akpabio da zama mai ƙara mai gabatar da ƙara kuma mai yanke hukunci duk shi daya, wanda hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp