Majalisar wakilai ta fara zaman gaggawan da ta tsara yi yau, Laraba domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar.
A farkon makon nan ne, majalisar ta sanar da katse hutunta na shekara da ta soma ranar 23 ga watan Yulin 2023 domin yin zaman.
Zaman na zuwa ne sa’oi kafin soma zanga-zangar da wasu ƴan Najeriya ke shirin yi domin nuna damuwa game da matsi da tsadar rayuwa da ake ciki a ƙasar.


