Majalisar Wakilai ta yi ƙarin bayani kan dalilin da ya sa take son a gyara kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, inda ƴan majalisar ke son cire hukuncin kisa ga mata masu ciki.
Ƴan majalisar dai na son sauya hukuncin kisan da hukucin ɗaurin rai da rai.
‘Yar majalisar wakilan Fatima Talba da ta fito daga jihar Yobe ta ce ƙudurin ya tsallake karatu na biyu, kuma dab yake da ya zama doka.
“Yanke hukuncin kisa ga uwa mai juna biyu ba daidai ba ne saboda ba a san me za ta haifa ba. Watƙila ta haifi yara biyu ko ɗaya to shi yaron ko yaran mene ne laifinsu?”.
“Gara ma a ce an yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai domin a yayin zamansu za a iya samun yanayin da wani gwamna zai iya zuwa ya yi musu afuwa.” In ji honorabul Fatima.


