Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da tabbatar da dimokradiyya a Najeriya, ta buƙaci shugabannin majalisun dokokin biyu, su yi watsi da kudirin lura da shafukan sada zumunta a
ƙasar.
Cikin wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar , a ce kudurin idan ya zaman doka, zai taƙaita ‘yancin faɗar albarkacin baki da ɓoye sirri.
SERAP ta buƙaci gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin shugaba Tinubu ta daina yunƙurin tilasta wa manyan kamfanonin fasaha na Google da Youtube taƙaita wannan ‘yanci na ɗan’adam.
Rahotonni sun ambato babban mataimakin daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, na cewa ƙudurin zai mayar da ”halastaccen ‘yancin ɗan’adam zuwa laifi”
Ya ƙara da cewa “duk wani yunƙuri na sanya idanu domin lura da shafukan sada zumunta, za mu ɗauke shi a matsayin abin da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin ‘yancin ɗan’adam na ƙasa-da-ƙasa.”
An dai daɗe ana ta kiraye-kiraye ga hukumomin ƙasar da su yi wata doka da za ta riƙa lura da abubuwan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, sakamakon yawaitar yaduwar labaran ƙarya da na cin zarafi a shafukan.


