Tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Neja, Abubakar Chika, ya ce, warewar da aka yi wa shugabancin Majalisar na da hadari ga dimokuradiyya.
Chika ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa, majalisa kungiya ce mai zaman kanta, don haka a bar ‘yan majalisar su zabi a tsakaninsu.
“Shugaban kasa ko jam’iyya ba su da hurumin tantance wanda ya dace ya jagoranci majalisar dokokin kasar. Ban ga wani dalili na microzone ba.
“Wannan rashin bin tsarin dimokuradiyya ne kuma yana da matukar hadari ga dimokuradiyya… Ba na son ganin an lalatar da wannan bangaren gwamnati a mulkin kama-karya”, in ji dan siyasar.
Chika ya ce jam’iyyar APC ta yi kaca-kaca saboda shawarwari daban-daban da ke fitowa daga bangarori da dama, inda suka yi kuskure wajen raba manyan kujeru a majalisar.
“Ya aka yi kuka cire yankin Arewa ta tsakiya, to ina ganin abin son zuciya ne? Wani yana tunanin dole ne in sanya wannan mutumin ko zai rufa min asiri.”
Tsohon dan majalisar ya kara da cewa ya yi imanin zababben shugaban kasa Bola Tinubu mutun ne mai daraja kuma “ya kamata ya yi tunani fiye da jihar Legas”.
“Wannan Najeriya ce ba majalisar dokokin Legas ba kuma muna da majalisar kasa da ta kunshi mutane daga ko’ina kuma masu halaye daban-daban.”
Chika ya tunatar da jam’iyyar APC cewa ba ta da rinjaye musamman a majalisar wakilai inda ‘yan tsiraru suka fi yawa.
Da yake lura da cewa doka ba ta ce dan jam’iyyar APC ne kadai ya zama shugaban majalisar ba, ya ce jam’iyyar na iya yin rashin nasara idan ta zama “matukar sakaci”.
Chika ya shawarci shugabannin jam’iyya mai mulki da su sake tunani, domin kasar ba a karkashin mulkin soja ba ce, a tsarin mulkin dimokradiyya.