Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Mainz ta soke kwantiragin Anwar El Ghazi ɗan ƙasar Holland saboda wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na goyon bayan Falasɗinawa a rikicin Isra’ila da Gaza, kamar yadda kulob ɗin ya tabbatar a ranar Juma’a.
Kulob ɗin na Bundesliga ya dakatar da ɗan wasan mai shekaru 28 a ranar 17 ga watan Oktoba bayan wani saƙon da yanzu ya goge a shafukan sada zumunta wanda ya nuna goyon bayan Falasdinawa.
A ranar Litinin, Mainz ta ɗage dakatarwar da aka yi masa tare da yi masa gargaɗi a hukumance.
Amma a ranar Juma’a, ƙungiyar ta sanar da cewa ta soke kwantiragin El Ghazi ”nan take”.
“FSV Mainz 05 tana kawo ƙarshen dangantakarta da Anwar El Ghazi kuma ta sallami ɗan wasan a ranar Juma’a. Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne a matsayin martani ga kalamai da rubuce-rubucen ɗan wasan a shafukan sada zumunta,” in ji Mainz.
A baya Mainz ta ce sakon El Ghazi ya ɗauki ”matsaya kan rikicin Gabas ta Tsakiya da ba ta daidaita da matsayar kulob ɗin ba.”
El Ghazi ya ƙulla yarjejeniya da Mainz a bazaran da ta wuce kuma ya buga wasanni uku a kakar wasa ta bana