Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar Zamfara sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴanbidida a jihar.
Matan waɗanda suka fito daga garin Jimrawa na yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda sun koka kan yadda suka ce ƴanbindiga na ci gaba da addabarsu da jerin hare-hare tare da sace musu mutane, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Zanga-zangar matan na zuwa aƙalla mako biyu bayan wasu zarga-zanga biyu da aka gudanar a brnin na Gusau, bayan da masu zanga-zangar suka yi iƙirarin cewa hare-haren ƴanbindigar sun kashe fiye da mutum 100 a ƙauyukan Mada da Ruwan Baure da fegin Baza da Lilo da kuma Bangi.
Ƙaramar hukumar Kaura Namoda na daga cikin ƙananan hukumomin jihar da hare-haren yanbindiga ke ci gaba da addaba.
Mazauna jihar sun ce rashin hanyoyi masu kyau na kawo wa jami’an tsaro tarnaƙi wajen isa yankunan, lamarin da ke bai wa ƴanbindigar dmar cin karensu babu babbaka.