Fitaccen attajirin nan Elon Musk ya sake ɗarewa kan matsayinsa na mafi arziki a duniya inda yake da dukiyar da ta kai dala biliyan 187, ya kuma zarce Bernard Arnault na Faransa.
Elon Musk ya kasance mamallakin kamfanin Tesla da ke ƙera motocin lataroni.
Baya ga Tesla, Musk ne babban jami’in SpaceX, kamfanin ƙera jiragen roka kuma yana da hannun jari a shafin sada zumunci na Tuwita.
A cewar wani rahoto na baya-bayan nan da Bloomberg Billionaires Index, ya fitar, ƙaruwar hannun jari da aka samu a Tesla ya taka rawa a sake komawarsa kan matsayinsa bayan da hannun jarin Tesla ya ƙaru da kashi 92 cikin 100.
Bloomberg Billionaires Index yana fitar da jadawalin mutanen da suka fi arziki a kullum kuma ana bayyana yawan arzikinsu a ƙarshen kowace rana a New York.
Yawan arzikin Musk ya yi ƙasa da sama da dala biliyan 200 tsakanin Nuwamba da Disambar shekarar da ta gabata, abin da aka bayyana a matsayin asara mafi girma da ya tafka a baya-bayan nan.
A watan Aprilun 2022, Musk ya yi tayin sayen Tuwita kan $44 billion inda kuma ciniki ya faɗa a watan Oktoban 2022.
Bayan da ya karɓi ragamar shugabancin Tuwita, Elon Musk ya rage sama da ma’aikata 3,700 kusan rabin ma’aikatan kamfanin.
A baya-bayan nan Tuwita ya sanar da matakin rage ma’aikata karo na takwas kuma an sallami fiye da mutum 50 a ƙarƙashin jagorancin Musk.