Emiliano Martinez ya lashe kyautar Yashin – ta gwarzon mai tsaron raga na 2024.
Wannan ce shekara ta biyu a jere da yake lashe wannan kyauta – yana buga kwallo a Aston Villa kuma ɗan asalin ƙasar Argentina.
Yayin da Rodri ɗan wasan Manchester City ɗan ƙasar Spain ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya.