Wani haɗarin mota da ya faru a Algeria ya halaka ɗan wasa da kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Mouloudia Club El Bayadh lamarin da ya tilastawa hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ɗage dukkan wasannin da aka tsara bugawa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ce mai tsaron ragar ƙungiyar Zakaria Bouziani mai shekara 27 da mataimakin koci, Khalid Muftah sun mutu sanadin haɗarin.
Ƴan wasan na hanyar zuwa Tizi Ouzou domin buga wasa da JS Kabylie ranar Juma’a lokacin da motar ɗauke da tawagar ƴan wasan ta yi haɗari kusa da birnin Tiaret da ke arewa maso yammacin Algeria, a cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar.
Shugaban Algeria, Abdelmajid Tebboune ta ce cikin wata sanarwa cewa ya samu rahoton ibtila’in tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan ƴan wasan da suka rasa ransu.
Ƙungiyar a saƙon da ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce sauran ƴan wasan da suka ji rauni ba sa cikin wani mummunan yanayi.
A cewar sanarwar, hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta yanke shawarar dakatar da duk wasannin da aka shirya yi a ƙarshen mako


