Wani mutum dan shekara 42 mai suna Ibrahim Adamu Mohd ya kashe kansa ta hanyar rataya a kan bishiya a unguwar Kanti da ke karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da mazauna garin Kanti suka tashi da safe, suka tarar da wani mutum da ba a san ko wanene ba, da igiya a wuyansa, yana rataye a jikin bishiya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin.
Ya ce wanda aka kashe din mai suna Ibrahim Adamu dan asalin kauyen Gayawa ne da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.
Ya ce, Mista Ibrahim ya kashe kansa ne ta hanyar rataya a kan titin Daura Road Adjacent Baushe a garin Kazaure a wani gini da bai kammala ba.
Shiisu ya ce an samu katin gayyata da katin SIM guda biyu a hannunsa.
Ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin mutuwarsa.