Pearl Ogbolu, ‘yar asalin Legas wacce aka fi sani da Erelu Okin, ta nemi afuwar ta na raba man fetur a matsayin abin tunawa a bikinta.
A ‘yan makonnin da suka gabata ‘yan Najeriya na fama da matsalar karancin man fetur, bayan da aka samu matsala a harkar samar da man fetur.
Kwanan nan wani faifan bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ke nuna ana rarraba man fetur a matsayin abin tunawa a taron Ogbolu na Legas.
Shagalin bikin wanda aka gudanar a ranar 4 ga Maris, ya jawo cece-ku-ce daga ‘yan Najeriya. A kuma ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin jihar Legas ta rufe Havilah Event Centre, inda aka gudanar da bikin, bisa laifin saba ka’idojin kare lafiyar jama’a.
Daga bisani, Abiodun Alabi, kwamishinan ‘yan sandan Legas, ya bayar da umarnin kamo wadanda ke da hannu wajen rabon kayayyakin ajiyar man fetur.
Adekunle Ajisebutu, mai magana da yawun ‘yan sandan Legas, ya sanar da ci gaban, inda ya bayyana abin da Ogbolu ta yi a matsayin “abin zargi”.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, Ogbolu ta ce: “Ina so in yi amfani da wannan kafar, domin neman afuwa kan yadda aka shigo da kayayyakin ajiyar man fetur cikin zauren bikin.
“Niyyata ita ce, kawai in nuna godiya ga baƙi na domin halartar taron na a cikin waɗannan lokutan wahala.
“Na dakata domin yin tunani da kuma ba da hakuri da gaske, kuma na gode muku duka, saboda fahimtar ku da sukar ku.” A cewar ta.
Tun da farko kwamishinan yada labarai Gbenga Omotosho ya ce jihar za ta binciki lamarin.