Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno, Isa Gusau, ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa Isa Gusau ya rasu ne a da yammacin ranar Alhamis a ƙasar Indiya bayan shafe lokaci yana jinya.
Gusau ya fara aikinsa na mataimaki kan harkokin yaɗa labarai ne tun lokacin tsohon gwamnan Borno, Kashin Shettima, mataimakin shugaban Najeriya a yanzu.
Bayan karewar wa’adin Shettima ne, gwamna Babagana Umara Zulum ya sake naɗa shi a matsayin mai magana da yawunsa a 2019, muƙami da ya riƙe har zuwa miutuwarsa.
Jama’a da dama dai ciki har da ƴan uwa da abokai ke ta alhinin rashinsa, inda aka bayyana shi a matsayin hazikin mutum kuma mai nagarta.