Daya daga cikin wadanda suka fi dadewa suna yi wa Masallacin Manzon Allah S.A.W hidima Agha Habeeb Muhammad al-Afari, ya rasu a yau Laraba.
Shafin Tiwita na HaramainSharafain ya ruwaito cewa Agha Habeeb shi ne ke kula da dakin da kabarin Mazon Allah S.A.W yake.
Tuni dai aka gudanar da jana’izarsa a masallacin Annabi (S.A.W) da ke Madina.