fidelitybank

Mai kuɗin duniya zai sayi shafin Twitter

Date:

Shugaban kamfanin ƙera motoci na Tesla kuma attajirin duniya, Elon Musk, ya yi tayin sayen dandalin sada zumunta na Twitter kacokam don ya “fito da” da baiwa ta musamman da kamfanin ke da ita.

Cikin wata sanarwa ta ban-mamaki, Mista Musk ya ce, zai biya dala 54.20 kan kowane hannun jari ɗaya, inda ya yi hasashen darajar dandalin kan dala biliyan 40.

A kwanan ne aka ruwaito cewa Musk ya zama mai mafi girman hannun jari a Twitter bayan ya ƙara yawan hannun jarinsa a kamfanin.

Ya ƙara da cewa idan ba a karɓi tayin da ya yi ba: “Zan yi tunanin sauya matsayina na mafi yawan hannun jari.”

Cikin bayanan, Musk ya ce ba ya son “je-ka-ka-dawo” sannan ya ce: “Tayi ne mai tsoka kuma masu hannun jarinku za su so shi.”

Zai ɗauki matakin sayar da hannun jarinsa idan har ba a karɓi tayin nasa ba, a cewarsa.

“Wannan ba barazana ba ce, kawai dai ba zai zama zuba jari kai waye ba idan ba a samu sauyin da ake buƙata ba,” in ji shi.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp