Ƴan bindigar da suka kai harin bom a jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna sun saki matar da ke da ciki daga cikin fasinjojin da suke garkuwa da su.
An sako matar ne saboda dalilai na jin-kai, kamar yadda Kwamishinan tsaro da harakokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya tabbatar wa BBC.
Sai dai ya ce har yanzu ba su ido biyu da matar ba, amma ya ce gwamnatin Kaduna a shirye ta ke ta kula da ɓangaren kiwon lafiyarta.
Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta wanda jaridar Daily Nigeria ta wallafa, ya nuna wata mata sanye da hijabi da takunkumin fuska tana bayanin cewa ita ce mai ciki daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa.
A cikin bayaninta ta ce: “Sun ji tausayi na sun sake ni saboda halin da nake ciki.”