Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila Gareth Southgate ya ajiye aikinsa bayan jagorantar tawagar zuwa wasan ƙarshe na gasar ƙasashen Turai karo biyu a jere.
Tawagar ta Three Lions ta sha kashi a hannun Sifaniya da ci 2-1 a wasan ƙarshen da suka buga ranar Lahadi, da kuma wanda Italiya ta doke su a bugun finareti shekara uku da suka wuce.
A ƙarshen shekarar nan ne kwantaragin kocin mai shekara 53 zai ƙare, inda ya ja ragamar ƙasar tasa ta haihuwa wasa 102 cikin shekara takwas.
“A matsayina na ɗan Ingila mai cike da alfahari, taka wa Ingila leda da kuma jagorantar ta alfarma ce a rayuwata,” in ji Southgate.
“Hakan ya fi komai a rayuwata, kuma na yi duk mai yiwuwa.
“Amma lokacin sauyi da kuma buɗe wani sabon babi ya yi.”


