Mai fafutikar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho, ya mayar da martani kan kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari na cewa, an kashe miliyoyin ‘yan Najeriya a yakin basasar Biafra domin tabbatar da hadin kan kasar.
Igboho ya yi gargadin cewa, ba za a taba barin irin wannan babban kisa ya sake afkuwa a Najeriya ba.
Buhari ya yi kira ga shugabannin siyasa da su maida hankali wajen tabbatar da manufar inganta muradun kasar nan.
Ya jaddada cewa kasar ba za ta iya sake samun wani yakin basasa ba.
Da yake mayar da martani, Igboho, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olayomi Koiki, ya fitar, ya ce: “Mun san shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ubangidan dukkan Fulani a duniya. Amma kasar Yarbawa ba za ta taba cin hannun Fulani ba.
“Shugaba Muhammadu Buhari yana tunatar da Nnamdi Kanu da ‘yan kabilar Igbo kisan kiyashin da suka yi a lokacin yakin Biafra. Ya kamata shugaban kasa ya sani cewa ba za a sake yin irin haka a kowace kasa tamu ba.
“Dukkanmu mun farka da shirin Fulani.”


