Dan wasa Riyad Mahrez ya sabunta kwantiragin shekaru biyu tare da zakarun gasar Premier Manchester City inda kwantiraginsa zai kare har zuwa 2025.
Tsohon kwantiragin Mahrez ya kamata ya kare ne a shekarar 2023 amma a yanzu dan wasan na Algeria ya kulla makomarsa a kungiyar da ya koma daga Leicester a kan fan miliyan 60 a shekarar 2018.
“Abin farin ciki ne kasancewa cikin irin wannan kulob mai ban mamaki.”
Mahrez, mai shekaru 31, ya ci kwallaye 77 a wasanni 254 na gasar Premier da ya buga wa Leicester da Manchester City.