Wani mahauci a jihar Adamawa ya kashe matarsa da wuka.
Wanda ake zargin mai shekaru 33, Ibrahim Abubakar, ya zargi matarsa mai suna Hajara Sa’adu mai shekaru 25 da daukar wayarsa kafin ya daba mata wuka har lahira.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce wanda ake zargin wanda ke zaune a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Girei ya daba wa marigayiyar wuka a bayanta.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:30 na safe, inda ya zarge ta da daukar wayarsa, zargin da ya janyo cece-kuce.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce mahaucin ya daba wa matarsa wuka kuma ya bar ta cikin jini.
Nguroje ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne bayan rahoton da mahaifin marigayin ya kai wa ‘yan sanda.
Ya kara da cewa binciken farko da aka yi ya kai ga gano wasu shaidun shaida a wurin da aka aikata laifin da wanda ake zargin ya yi amfani da shi wajen aikata laifin.
Ya ce wanda ake zargin da kan sa ya amsa laifinsa kuma ya bayyana nadamar kashe matarsa da mahaifiyar ’ya daya tilo da suka haifa.
“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Dankombo Morris, yayin da yake nuna rashin jin dadinsa game da lamarin, ya tabbatar da cewa rundunar za ta tuhumi mai laifin,” in ji Nguroje.