A karon farko, ‘yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan fasinja da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun yi jawabi, inda suka yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.
A jiya ne, wani bidiyo da ya bayyana, ya nuna wasu daga cikin maharan ɗauke da bindigogi suna iƙirarin cewa su ne suka sace fasinjojin jirgin ƙasan a ranar Litinin din makon jiya.
Bidiyon, wanda bai kai tsawon minti 1:30 ba, ya nuna huɗu cikin ‘yan bindigar sanye da kakin sojoji, rufe da fuskoki a tsaye suna iƙirarin ci gaba da riƙe fasinjojin jirgin ƙasa da suka sace a ƙarshen watan jiya.
Ba a dai ga fasinjojin a cikin taƙaitaccen bidiyon ba, amma mutanen da suka yi maganar sun tabbatar da cewa suna riƙe da su.