Kashi na farko na mahajjata 510 daga Borno, za su tashi zuwa Madina ranar Juma’a zuwa Makka don fara gudanar da babban aikin Hajji.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ba da rahoton cewa, za a jigilar mahajjatan a cikin motocin alfarmab, isa bin ka’idojin COVID-19.
Wani jami’i a cibiyar kula da harkokin Madina ya shaidawa NAN cewa mahajjatan za su fara aikin Hajjin ne daga Miqat Hulifa.
Hulifa yana da nisan kilomita tara daga Madina, kuma yana da nisan kilomita 450 daga Makka.
Shi ne Meeqat ga mutanen da suke fitowa daga Madina.
Meeqat ita ce babbar iyakar da mahajjata masu niyyar zuwa aikin Hajji ko Umra za su shiga cikin Ihrami.
Ihrami yanayi ne na keɓe wanda aka haramta wasu ayyuka da aka halatta a cikinsa.