Hukumar kula da alhazai ta kasa NAHCON, ta ce masu son zuwa aikin Hajji na shekarar 2022 za su biya kusan naira miliyan biyu da rabi.
A cewar hukumar, mazauna yankin Arewacin Najeriya za su biya jumillar kuɗi Naira 2,449,607.89, yayin da na yankin Kudu za su biya 2,496,815.29.
Mazauna jihohin Borno da Yola kuma za su biya 2,408,197.89, a cewar hukumar.